15 Satumba 2020 - 12:14
​Iraki : An Dakile Wani Harin Daesh A Kudancin Samira

Mayakan rundunar Hashdu-ashabi ta kasar Irak a Larandin salahuddin sun sami nasarar wargaza shirin mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh na kai hare-hare a kan wasu wurare a birnin Samira a cikin lardin.

ABNA24 : Majiyar muryar JMI daga birnin Bagdaza ya nakalto majiyar rundunar tana cewa hakan ya auku ne a yankin Tal Zahab daga kudancin birnin Na Samira a safiyar yau Litinin. Har’ila yau wata majiyar jami’an tsaron kasar ta Iraqi ta bada sanarwan cewa hadin guiwar jami’an tsaro a garin na Samira sun sami nasarar kashe wasu dakarun na kungiyar Daesh gud 4, daya daga cikinsu ya yi damara da boma-bomai.

Tun shekara ta 2017 ne aka kawo karshen ikon kungiyar ta Daesh a arewacin kasar Iraqi amma har yanzun akwai wasunsu a boye a cikin kasar kuma suna shirye-shiyen kai hare-hare a wasu wurare a kasar.

342/